Matan da aka sace sun samu jarirai da juna biyu daga ƴan ta’addan jihar Neja 

0
15

Wasu daga cikin matan da aka sace a cikin watan Fabrairun 2024 daga ƙauyukan da ke ƙananan hukumomin Rafi da Shiroro a Jihar Neja sun kuɓuta daga hannun ‘yan ta’adda, inda suka dawo da ciki da kuma jariran da suka haifa a lokacin da suke hannun yan ta’addan.

Rahotanni sun nuna cewa ciki da jariran da suka dawo da su mallakin ‘yan ta’addan ne waɗanda suka yi musu sama da shekara guda kafin jami’an ‘yan sanda su ceto su mako guda da ya gabata.

An gano cewa huɗu daga cikin matan na cikin mutum 25 da aka sace a yankin Allawa a kan hanyar Pandogari-Allawa yayin da suke dawowa daga kasuwa a watan Fabrairun 2024.

Bayanai sun nuna cewa ‘yan ta’addan na amfani da motocin haya wajen jigilar kusan mata 24 daga kauyen Palu-Waya da ke ƙaramar hukumar Shiroro zuwa wani wuri na daban.

Wasu majiyoyi, ciki har da na ‘yan sanda, sun bayyana cewa ana shirin kaisu Jihar Kebbi, yayin da wasu suka ce ana tura su ne zuwa dajin Kaiji da ke ƙaramar hukumar Borgu, inda ‘yan ta’addan suka umurci direban da ya kai su.

Bayan sun isa garin Kagara da ke ƙaramar hukumar Rafi, ɗaya daga cikin matan ta nemi izinin sauka don yin fitsari, a lokacin ne ta yi ƙarar neman agaji, lamarin da ya janyo sanadiyar ceto su tare da kama direban, wanda yanzu haka yana tsare a hannun ‘yan sanda.

Majiyar ‘yan sanda ta shaida wa Daily Trust cewa ana tsare da matan a hedikwatar ‘yan sanda da ke Minna. Haka kuma, an gano tarin alburusai a cikin jakar ɗaya daga cikin matan da aka ceto.

Bugu da ƙari, majiyar ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto tana cikin ‘yan matan Chibok da aka dade da nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here