Kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya kadarorin da aka rasa mamallakin su

0
6

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta samu nasarar ƙwace wasu kadarori da suka haɗa da gidaje, filaye, gidajen mai da asusun ajiya na banki da ke ɗauke da sama da Naira miliyan 333, waɗanda yanzu sun koma mallakin Gwamnatin Tarayya.

A cewar sanarwar da EFCC ta fitar a shafinta na X, babbar Kotun Tarayya da ke Maitama a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Emeka Nwite, ita ce ta bayar da wannan umarni a ranar 14 ga Yuli, 2025.

Daga cikin kadarorin da aka ƙwace har da asibitin Galaxy Hospital, da kuma gidajen mai guda biyar da ke cikin jihohin Kaduna, Borno da Maiduguri. Haka kuma, akwai gidajen zama, gonaki da filaye dake babban Birnin Tarayya, Borno, Nasarawa da Jihar Neja.

Haka nan, kotun ta ƙwace asusun ajiyar banki na kamfanoni kamar su Galaxy Transportation and Communication Service Ltd, Galaxy Computing and Electronics Service Ltd, da Galaxy Energy International Concept Ltd, waɗanda jimillar kuɗaɗensu ya kai fiye da Naira miliyan 333.

EFCC ta bayyana cewa ta gabatar da ƙarar neman wannan ƙwacewar bisa hujjoji da ke cikin shaidar rantsuwa mai shafuka 36, inda ta nuna cewa kadarorin da kuɗaɗen na da alaƙa da ayyukan da ake zargin sun saba wa doka.

A baya kotu ta bawa EFCC umarnin yin shelar kadarorin a jaridu, wanda aka rasa wanda zai fito ya bayyana cewa shine mamallakin kadarorin, haka ne kuma ya bawa kotun damar bawa gwamnatin tarayya umarnin kwace ikon kadarorin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here