Gwamnatin tarayya ta dakatar da ɗaukar sabbin ma’aikatan hukumomin tsaro

0
9

Bangaren dake kula da harkokin hukumomin tsaron a’lumma Civil Defence, masu kashe gobara, da masu kula da gidajen gyaran hali, ya dakatar da shirin daukar sabbin ma’aikata saboda yawan mutanen da aka samu suna neman aikin.

A wata sanarwa da Sakataren Hukumar, Manjo Janar AM Jibril (mai ritaya), ya fitar a ranar Laraba a birnin Abuja, ya bayyana cewa an yanke wannan shawara ne domin a inganta yadda tsarin ke aiki da kuma tabbatar da cewa an gudanar da aikin ɗaukar ma’aikata cikin sauƙi da tsari a dukkan hukumomin da abin ya shafa.

Jibril ya ce rufe shafin a yanzu yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin tantancewa.

 Ya kuma tabbatar wa da masu neman aikin cewa za’a buɗe shafin a ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025. Ya shawarci masu sha’awar aikin su kasance cikin shiri domin mika takardunsu da wuri idan bukatar hakan ta taso.

Hukumomin da wannan mataki ya shafa sun haɗa da:

Hukumar Tsaron Ƙasa da Ƙasa (NSCDC)

Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS)

Hukumar kashe gobara (Federal Fire Service)

Hukumar Gidajen Yari ta Ƙasa (NCoS)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here