Dele Momodu ya fice daga jam’iyyar PDP

0
8

Fitaccen ɗan siyasa kuma ɗan jarida mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar  PDP a hukumance, yana mai zargin cewa jam’iyyar ta fita daga turbar da aka kafa ta akai.

A cikin wata wasika mai kwanan wata 17 ga Yuli, 2025, da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na mazaɓar Ihievbe, ƙaramar hukumar Owan a Jihar Edo, Momodu ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar nan take.

A cewarsa, jam’iyyar PDP ta shiga hannun wasu ‘yan ƙungiyoyi marasa kishin dimokuraɗiyya daga ciki da wajen jam’iyyar, lamarin da ya sa ya zama da wuya a ci gaba da bin gaskiya da adalci a harkokin cikin gida na jam’iyyar.

“Dalilina abu ne mai sauƙi kuma a bayyane yake. An kwace jam’iyyarmu ta hanyar wasu miyagun ƙungiyoyi masu adawa da dimokuraɗiyya,” in ji shi a cikin wasikar.

Saboda haka, abu ne mai kyau a bar ragowar jam’iyyar a hannunsu yayin da yawancinmu muke komawa sabuwar haɗakar ADC, in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here