Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta bayyana ta gano wasu makarantu da suka bayar da gurbin karatu ga ɗalibai 9,469 ba bisa ka’ida ba a shekarar 2024.
A cewar JAMB, wannan karɓar dalibai an yi su ne ba tare da amfani da tsarin da aka ƙirƙira domin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin karɓar dalibai a Najeriya.
Tsarin yana baiwa ɗalibai damar lura da matsayin shigarsu makaranta tare da tabbatar da cewa an bi duk ƙa’idoji na karɓar ɗalibai.
Makarantun da aka fi samun adadin waɗanda aka karɓa ba bisa ka’ida ba sun haɗa da,
Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote Kano – 2,215
Jami’ar Ladoke Akintola – 1,215
Jami’ar Jihar Gombe – 1,164
Jami’ar Emmanuel Alayande ta Koyar da Malamai – 761
Jami’ar Fasaha ta Tarayya Owerri – 534
Jami’ar Ambrose Alli – 514
Jami’ar Igbinedion – 365
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Akwa Ibom – 340
JAMB ta ja kunnen makarantu da su daina karɓar ɗalibai ta hanyar da ba ta dace ba.
Hukumar ta gargadi cewa irin wannan aiki zai iya janyo mummunan sakamako ga ɗalibai da makarantu.
Daga ciki akwai yiwuwar hana ɗaliban da abin ya shafa halartar hidimar ƙasa ta NYSC, tare da ɗaukar matakin doka kan makarantu da mutanen da suka aikata hakan.