Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP

0
12

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓukan 2019 da 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na mazaɓar Jada 1 da ke ƙaramar hukumar Jada a jihar Adamawa.

 Wasiƙar, wadda aka sanyawa hannu a ranar 14 ga Yuli, an tabbatar da ingancinta daga ɗaya daga cikin jami’an yaɗa labaran Atiku.

A cikin wasiƙar, Atiku ya bayyana cewa dalilin ficewarsa shi ne ganin jam’iyyar PDP ta kauce daga ainihin manufofin da suka kafa ta a kai.

“Ina rubuta wannan wasiƙa ne domin sanar da ficewata daga jam’iyyar PDP daga yau ɗin nan,” in ji Atiku.

Yanzu haka Atiku na jagorantar haɗa kan shugabannin ‘yan adawa domin fafatawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here