Ana zaman zulumi a unguwar Ebute Meta da ke Jihar Legas, biyo bayan wani jerin hare-hare masu tayar da hankali da ake kyautata zaton suna da nasaba da rikicin ƙungiyoyin asiri, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku a cikin kwana biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne ranar Lahadi, inda aka kashe wani matashi da aka fi sani da Agbara a kan titin Lagos, bayan wasu da ba a san ko su wane ba suka far masa, sannan suka kashe shi. Wannan hari ya tayar da hankalin mazauna yankin matuƙa.
Bayan awa 24 da faruwar hakan, sai aka sake samun kashe wasu biyu. An harbe wani da ake kira Butcher da safiyar ranar Litinin, sannan daga bisani wani ma’aikacin mai gyaran famfo wanda ba a gano sunansa ba aka tsinci gawarsa da raunin sara da adda.
Wasu daga cikin mazauna unguwar na danganta rikicin da takaddama tsakanin ƙungiyoyin asiri masu adawa da juna da ke fafatawa a yankin.
Hukumomin ‘yan sanda a jihar Legas sun ce sun fara ɗaukar matakan dakile ci gaba da yaduwar wannan fitina.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa an tura jami’an sashen yaƙi da ƙungiyoyin asiri zuwa dukkan sassan yankunan da lamarin ya faru domin dakile rikicin kafin ya kai mummunan matakin da za’a gaza magancewa.