Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta wanke tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, daga dukkan tuhume-tuhumen da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar da shi dangane da zargin almundahanar kuɗi.
An yanke hukuncin ne a safiyar ranar Talata, wanda hakan ya kawo ƙarshen shari’ar da ta ɗauki shekaru da dama tana gudana.
Fayose, wanda aka zarga da karkatar da kuɗaɗen jama’a yayin mulkinsa, ya sha musanta zargin tun farko. EFCC ta ce Fayose ya yi amfani da kuɗaɗen da suka kai daruruwan miliyoyin naira ba bisa ka’ida ba, zarge-zargen da suka jawo hankalin ’yan ƙasa kuma suka mamaye mahawarar siyasa na tsawon shekaru.
Sai dai kotun ta amince da bukatar lauyoyin Fayose na cewa babu wata hujja da za ta sa a ci gaba da shari’ar, tana mai cewa EFCC ta kasa bayyana hujja mai ƙarfi da za ta tilasta wa wanda ake tuhuma amsa laifin da ake zargin ya aikata.