Gwamnatin Kano tayi rijistar mutane miliyan 7 a shirin tallafawa masu ƙaramin ƙarfi

0
13

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta yi rijistar mutane sama da miliyan 7 a cikin kundin bayanan shirin tallafi, domin sauƙaƙawa marasa karfi da tabbatar da adalci wajen rarraba tallafi a fadin jihar.

Shugaban kwamitin tsare-tsaren tallafin, Abdulmumin Ajumawa, ya ce an samo mutanen daga gidaje miliyan 1.7 a ƙananan hukumomi 44 na Kano. Ya bayyana rijistar a matsayin abin dogaro da za a yi amfani da shi wajen tantance wadanda suka cancanci tallafi, ba tare da nuna bambancin siyasa ba.

Ya ce ana gudanar da bincike don tabbatar da sahihancin bayanan da suka haɗa da lambar NIN, lambobin waya, da asusun banki. Wannan ya biyo bayan matsalolin da suka taso daga tallafin da bai samu tantancewa ba a baya.

Sabbin sauye-sauye a mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da suka haɗa da kafa Ma’aikatar Jinƙai da Hukumar Kariya ta KASPA, ne ya sa ake duba sabunta manufofin tallafin, inji shi.

UNICEF ta goyi bayan taron nazari da aka shirya na tsawon kwana biyu domin duba inganta shirin tallafi a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here