Gwamnatin Kano Ta Fara Bincike Kan Mutuwar Ɗalibai Biyu a Makarantar Kwana

0
15
Abba Gida Gida
Abba Gida Gida

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da bincike kan mutuwar wasu ɗalibai biyu a makarantar sakandare ta kwana da ke Bichi, bayan da aka zargi wasu abokan karatun daliban da kai musu hari.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Makoda, ne ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, domin gano gaskiyar abin da ya faru da kuma tabbatar da adalci ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

Ɗaliban da suka rasu su ne Hamza Tofawa da Umar Dungurawa, kuma rahotanni na nuna cewa wasu manyan ɗalibai ne suka kai musu hari da wani ƙarfe mai suna “Gwale-Gwale”.

Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Kiru, ya fitar ta ce an fara bincike domin gano hakikanin musabbabin rasuwar ɗaliban.

Babban Sakataren Ma’aikatar, Bashir Muhammad, wanda ya wakilci kwamishinan yayin da ya kai ziyarar gani da ido zuwa makarantar, yace gwamnati za ta tabbatar da gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci.

“Kar ku ɗauki doka a hannunku. Idan wani abu ya faru, ku sanar da malamai ko shugabannin makaranta domin daukar matakin da ya dace,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here