Dangote Zai Rage Farashin Gas Din Girki, Yan Kasuwa Sun Yi Allah-wadai Da Hakan

0
14
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana shirin rage farashin gas din girki (LPG) da kuma yiwuwar sayar da shi kai tsaye ga jama’a, idan masu rarraba kaya suka gaza sauke farashin. Ya ce gas din na da tsada wanda talaka ke gaza samun damar siya domin yin amfani dashi.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙi a matatar man sa da ke Lekki, inda ya ce yanzu haka suna samar da ton 22,000 na LPG a rana. Ya ce za su kara haɓɓaka samar Gas ɗin domin yayi daidai da bukatar ‘yan Najeriya.

Sai dai wasu masu ruwa da tsaki a harkar LPG, ciki har da Godwin Okoduwa, sun yi suka kan wannan shiri, suna cewa akwai danniya a tsarin. Sun ce kasuwa tana samun ci gaba ne ta hanyar haɗin gwiwa, ba ta hanyar danniya ba.

A yanzu ana sayar da gas tsakanin Naira 1,000 zuwa Naira 1,300 kowanne kilo, amma Dangote ya ce za su rage farashin domin sauƙaƙawa jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here