Shugaban Kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa nahiyar Afirka ta zama wuni dandalin siyar da man fetur mara inganci ga al’umma saboda dogaro da shigo da shi daga ƙasashen waje.
Dangote ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, kamar yadda wata sanarwa da aka fitar ranar Talata ta bayyana.
Da yake bayani kan dalilin gina babbar matatar man Dangote, attajirin ya ce burinsa shi ne ganin Najeriya ta samu isasshen mai da aka tace a cikin gida, da kuma farfado da irin wannan yunƙuri a sauran sassan Afirka, duk da ƙalubalen dake tattare da hakan.
“Ana shigo da mai a kusan dukkanin ƙasashen Afirka banda Aljeriya da Libiya da ke da isasshiyar matatar mai,” in ji Dangote.
Ya ce hakan yana faruwa ne duk da yawan danyen mai da Afirka ke da shi, lamarin da ke nuna bukatar gaggauta gina matatun mai masu inganci a nahiyar.
Dangote ya bayyana cewa da dama daga cikin mutane sun yi shakku cewa kamfaninsa zai iya kammala irin wannan babban aiki na gina matatar Mai. Wasu ma sun ba shi shawarar ya dakatar da aikin, suna danganta hakan da gazawar da wasu ƙasashe suka yi wajen kammala makamancin wannan aiki.