Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 27 a Wani Hari a Filato

0
11

Akalla mutum 27 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a unguwar Bindi-Jebbu da ke yankin Tahoss, a Karamar Hukumar Riyom ta Jihar Filato.

Rahotanni sun ce maharan sun afka wa al’ummar ne cikin daren Lahadi, inda suka bude wuta kan manoma da ke yankin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mata da maza da kuma kananan yara.

Wasu da dama sun jikkata sakamakon harin, inda aka garzaya da su tare da gawarwakin mamatan zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos domin samun kulawar gaggawa.

Rahotonni sun tabbatar da cewa harin ya bar al’umma cikin tsananin fargaba da alhini, musamman ganin yadda aka kashe mutane ba tare da kakkautawa ba.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here