Shugabannin Afirka Za Su Halarci Jana’izar Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari a Daura
Wasu daga cikin manyan shugabannin ƙasashen Afirka na daga cikin waɗanda ake sa ran za su halarci jana’izar marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, da za a gudanar yau Talata a mahaifarsa Daura, Jihar Katsina.
Shugabannin da ake tsammanin zuwansu sun haɗa da shugaban ƙasar Gambiya, Adama Barrow; shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Déby; da kuma shugaban ƙasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló.
A wani ɓangare kuma, tsohon shugaban ƙasar Ghana, Nana Akufo Addo, ya ziyarci iyalan marigayin a birnin Landan jiya Litinin domin yin ta’aziyya kafin a turo gawar zuwa Najeriya.