NSCDC Ta Tura Jami’ai 2,807 Don Tabbatar da Tsaro a Jana’izar Buhari a Katsina

0
12

Shalkwatar rundunar tsaron farin kaya ta ƙasa (NSCDC) reshen jihar Katsina ta bayyana cewa ta tura jami’anta 2,807 zuwa wurare masu muhimmanci a fadin jihar, domin tabbatar da tsaro kafin, lokacin da kuma bayan jana’izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da za a gudanar ranar Talata.

Kwamandan rundunar a jihar, Malam Aminu Datti, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina ranar Litinin.

Ya ce an dauki matakin ne bisa umarnin babban kwamandan rundunar NSCDC na kasa, Ahmed Abubakar Audi, wanda ya bukaci a tabbatar da cikakken tsaro a duk matakan jana’izar.

Malam Datti ya ce an tura jami’an tsaron ne zuwa wurare kamar birnin Daura, filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, fadar na sarakunan Katsina da Daura, da sauran wuraren da ake ganin suna da muhimmanci yayin jana’izar.

Ya kara da cewa wasu daga cikin dabarun da rundunar za ta bi sun hada da tsauraran sintiri, tattara sahihan bayanan sirri, hada kai da al’umma da kuma aiki tare da sauran hukumomin tsaro.

“Dukkan jami’ai na ɓoye da na fili da ke fadin jihar an umurce su da su kare dukkan muhimman ababen gwamnati,” in ji shi.

Kwamandan ya kuma umurci shugabannin sassa da rundunoni, daga matakin yanki zuwa na unguwanni, da su tabbatar da cikakken shiri da kuma zagayawa domin tabbatar da tsaro a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here