Daliban Sakandare A Sokoto Sun Kera Mota Mai Amfani da Lantarki

0
13

A wani ci gaba mai ban mamaki da ya ja hankalin kasa baki ɗaya, daliban makarantar Brilliant Footsteps International Academy da ke Jihar Sokoto sun ƙera mota mai amfani da lantarki, abin da ke zama babban ci gaba a fannin ilimi da fasaha a Najeriya.

An sanya wa motar suna BMT 1.0, inda ƙungiyar dalibai 15 ’yan ajin karshe (SS3) suka ƙirƙira, suka tsara kuma suka haɗa motar gaba ɗaya. Daliban sun haɗa da mata goma da maza biyar, kuma aikin ne na ƙarshe kafin kammala karatun su.

Rahoton Arewa PUNCH ya bayyana cewa wannan aiki na farko irinsa daga daliban sakandare a Arewacin Najeriya yana kara haskaka burin Najeriya na dogaro da kai a fannin kere-kere, dorewar ci gaba da kuma ’yancin masana’antu.

“Wannan ba kawai aikin makaranta ba ne saƙo ne,” in ji Dr. Shadi Sabeh, mai makarantar, a lokacin da aka bayyana motar a bainar jama’a.

Shugaban ƙungiyar ƙirƙirar motar, Ahmed Sadi, ya bayyana cewa sun gudanar da aikin kamar ƙungiyar injiniyoyi mai girma. “Kowane ɗalibi na da aikin da yake yi, daga walda, haɗa igiyoyin wuta, shigar da batir har zuwa gwajin tuki. Mun koyi aikin ta hanyar aikatawa,” in ji shi.

Daya daga cikin jagororin aikin, Aisha Ahmed, ta bayyana da kwazo da hangen nesa cewa tana cewa wannan mota hujja ce cewa kere-kere na iya faruwa a wuraren da ake rainawa. Idan aka ci gaba da wannan aiki kuma aka inganta shi, zai rage dogaro da Najeriya ke yi da shigo da motoci daga ƙasashen waje, tare da ƙarfafa sufuri mai ɗorewa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here