An kammala binne gawar binne gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a gidan sa dake Daura, jihar Katsina.
An binne Buhari kwanaki biyu bayan rasuwar sa a birnin Landan na kasar Birtaniya, inda yayi jinya a wani asibiti.
Jana’izar ta samu halartar manyan mutane daga cikin Najeriya da wajen ta.