Sheikh Aminu Daurawa, ya roƙi yan Najeriya su yafewa Buhari

0
12

Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yafewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tare da yi masa addu’ar samun rahamar Allah.

Sheikh Daurawa ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, bayan rasuwar Buhari da ta faru a yammacin jiya, Lahadi.

Malamin ya nemi hakan a daidai lokacin da al’umma ke bayyana mabanbantan ra’ayoyi akan mutuwar tsohon shugaban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here