Sarki Sanusi Ya Halarci Gasar Polo ta Bankin Access a Landan

0
9

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya halarci gasar Polo ta Access Bank a Surrey, London, inda ya hadu da tsohon kocin Chelsea kuma kocin Ingila, Thomas Tuchel, da wasu fitattun mutane daga sassa daban-daban na duniya.

Gasar, wadda ake kira Khalifa’s Cup, an saba gudanar da ita tun kusan shekaru goma da suka wuce, sannan ta samu halartar manyan baki ciki har da Gwamnan Katsina, Dikko Radda, da na Neja, Umar Bago. An yi amfani da taron wajen tara kuɗin gina ajujuwa da tallafa wa ilimi a Arewacin Najeriya.

Wani hoto da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna Sanusi da Tuchel suna tattaunawar barkwanci kan ƙungiyar Arsenal da cin kofin zakarun Turai.

 Sanusi ya bayyana kansa a matsayin masoyin Arsenal, yayin da Tuchel ya ce Arsenal ta siyo É—aya daga cikin tsoffin ‘yan wasansa, Noni Madueke.

Taron ya haɗa bayyana al’adu, wasanni da diflomasiyya, tare da nuna rawar da fitattun mutane ke takawa wajen tallafawa ci gaban al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here