Sai ranar Talata gawar Buhari zata iso Najeriya–Gwamna Radda

0
12

Sai ranar Talata gawar Buhari zata iso Najeriya–Gwamna Radda

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa ana sa ran gawar marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, za ta iso Najeriya ranar Talata mai zuwa.

Gwamna Radda ya sanar da hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Katsina. Ya ce jirgin da ke ɗauke da gawar marigayin zai sauka a jihar Katsina da misalin ƙarfe 12 na rana.

Ya ƙara da cewa za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 2 na rana a garin na Daura, inda za a binne shi bisa tsarin addinin Musulunci.

Buhari dai ya rasu a ranar Lahadi da yamma a wani asibiti dake birnin Landan a ƙasar Birtaniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here