Akalla mutum uku ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu bakwai aka ceto su da ransu bayan wani ginin bene mai hawa uku ya rushe a unguwar Abedi da ke Sabon Gari, cikin birnin Kano.
Ginin ya kasance wanda ya rushe kafin akai ga kammala shi a daren Lahadin data gabata, sannan ya shafi wasu gine-gine da ke kusa da wurin.
Jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Hukumar kashe gobara ta Tarayya da ta Jihar Kano, Hukumar Ƙiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), da ƴan sanda sun isa wurin domin gudanar da aikin ceto da tabbatar da tsaro.
Hukumomi sun bayyana cewa akwai yiwuwar wasu mutane na ci gaba da kasancewa a cikin tarkon baraguzan ginin, inda ayyukan ceto ke ci gaba da gudana.