Majalisun dokokin ƙasa sun dakatar da dukkan ayyukan su domin girmama rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a birnin Landan na ƙasar Burtaniya.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Majalisar, Kamoru Ogunlana, ya fitar a ranar Litinin daga birnin Abuja, ya bayyana cewa shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai suna cikin alhini dangane da wannan rashi mai girma.
“Domin nuna girmamawa ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, an dakatar da duk ayyukan Majalisar har zuwa Talata, 22 ga Yuli, 2025,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai sun umarci dukkan ‘yan majalisa da su daidaita shirye-shiryensu domin su samu damar halartar jana’izar marigayin.
Majalisar ta kuma miƙa sakon ta’aziyya ga Gwamnatin Tarayya, al’ummar Najeriya, Gwamnatin Jihar Katsina, da iyalan marigayin, inda ta bayyana Buhari a matsayin jagora mai kishin ƙasa da jajircewa wajen ɗorewar haɗin kan Najeriya.
“Shugaba Muhammadu Buhari zai ci gaba da kasancewa a zuciyar ‘yan Najeriya bisa irin sadaukarwarsa da gaskiyarsa.
Muna roƙon Allah Ya jikansa da rahama, Ya saka masa da Aljannatul Firdaus,” in ji sanarwar.