Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun girmama marigayi Buhari

0
17

Gwamnatin tarayya ta ayyana Talata, 15 ga Yuli, a matsayin ranar hutun girmamawa ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan, ƙasar Birtaniya.

Hutun na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na mako guda na jimamin kasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da shi tun da farko domin karrama Buhari.

Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Litinin.

Tunji-Ojo ya bayyana cewa hutun na musamman alama ce ta girmamawa bisa gudunmawar da Buhari ya bayar wajen tabbatar da dimokuraɗiyya da ci gaban Najeriya.

A cewarsa “Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Najeriya hidima da jajircewa, gaskiya, da kishin ƙasa, yana mai ƙoƙarin haɗa kan al’umma da kawo ci gaba ga ƙasar nan.”

Hutun zai bai wa ‘yan Najeriya dama su tuna da rayuwarsa, irin shugabancinsa, da ƙa’idojin da ya tsaya kai da fata wajen aiwatarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here