Dillalan  Mai Sun Goyi Bayan Sayar da Matatun Najeriya Da Rage Farashin Fetur

0
12
man fetur
man fetur

Ƴan kasuwar fannin mai da masana harkar fetur sun nuna goyon bayansu ga shirin sayar da matatun mai na Port Harcourt, Warri da Kaduna, waɗanda ke ƙarƙashin kulawar NNPCL. Sun buƙaci a aiwatar da shirin cikin gaskiya da adalci, tare da neman a rage farashin man.

Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari, ya ce matatun sun gaza samar da abuna ake bukata duk da kuɗin da aka zubawa gyaran su, saboda tsufan kayan aikin. Ya bayyana cewa ana sake nazarin makomar matatun, ciki har da yiwuwar sayar da su, amma ba a yanke shawara ba tukuna.

Masana sun ce sayar da matatun na iya kawo ƙarshen asarar kuɗin gwamnati, yayin da wasu ke nuna damuwa kan dalilin da yasa ake kawo wannan shiri a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here