Ana zaton dasa bama-bamai a kasuwar Waya ta Bata dake Kano

0
13

Ana zaman fargaba a Kasuwar Wayoyi dale Bata a jihar Kano, bayan da wasu da ba a san ko su wanene ba suka aike da saƙon barazanar tada bama-bamai a cikin kasuwar.

Shugaban kasuwar, Alhaji Mahrazu Usman Lawan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga kafar Arewa Update, inda ya bayyana cewa an fara aika masa da saƙon barazana tun daga yammacin ranar Lahadi.

A cewarsa, masu barazanar sun nemi a basu naira miliyan goma domin kaucewa tada bama-bamai a kasuwar, tare da bayyana cewa sun rigaya sun ɗaura abubuwan fashewa a shaguna guda bakwai.

Nan da nan shugaban kasuwar ya sanar da hukumomin tsaro, inda aka soma bincike tare da ƙara sa ido kan harkokin a’lumma a kasuwar.

Daga baya kuma, masu barazanar suka ci gaba da kiran waya kai tsaye.Alhaji Mahrazu ya ce jami’an tsaro sun gudanar da bincike sosai a kasuwar, amma ba su samu wata na’urar fashewa ba.

Hakan ne ya sa aka buɗe kasuwar a ranar Litinin har zuwa ƙarfe 5 na yamma.

Sai dai ya ƙara da cewa har zuwa tsakiyar ranar Litinin, masu barazanar na ci gaba da aika saƙonni, inda suka ce a jira dare domin ganin abin da zai faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here