Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan ya kwashe makonni biyu a ziyarar aiki zuwa ƙasashen Saint Lucia da Brazil.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Tinubu ya bar Najeriya tun ranar 28 ga Yuni, 2025 domin wata ziyarar aiki. A Saint Lucia, Shugaban ya tattauna batutuwan da suka shafi ƙarfafa dangantaka da ƙasashen yankin Caribbean da kuma karfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen kudancin duniya.
Daga bisani, a ranar 4 ga Yuli, ya wuce Brazil inda ya halarci taron ƙungiyar BRICS na shekarar 2025, wanda aka gudanar daga 6 zuwa 7 ga watan Yuli.