SERAP Tayi Karar NNPC Kan zargin wawure Naira biliyan 825 da Dala Biliyan 2.5

0
13

Kungiyar SERAP ta kai ƙarar NNPCL bisa zargin batar da makudan kuɗaɗen da aka ware don gyaran matatun mai, tare da gargaɗin cewa hakan na haifar da talauci da koma baya ga tattalin arziki.

An shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, bisa rahoton babban mai binciken kuɗi na Ƙasa na shekarar 2021, wanda aka fitar a watan Nuwamba 2024. 

Rahoton ya nuna akwai yiyuwar an batar ko an karkatar da kuɗaɗen da aka ware don muhimman ayyukan masana’antun man fetur na ƙasar nan.

SERAP ta ce maganganun attajiri Aliko Dangote da suka nuna cewa matatun man Najeriya na iya daina aiki gaba ɗaya, duk da biliyoyin dalolin da aka kashe wajen cewa ana gyara su, ya ƙara tabbatar da rashin gaskiya a harkar gyaran Matatun.

Kungiyar ta ce rashin bincike da dawo da waɗannan kuɗaɗe yana janyo talauci da koma baya ga tattalin arzikin ƙasa, tare da wargaza yunkurin wanzar da gaskiya da riƙon amana a fannin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here