Manyan Jami’an Tsaro Za Su Halarci Taron DICAN a Abuja

0
12

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, da Babban Hafsan Tsaro na Ƙasa, Janar Christopher Musa, za su kasance cikin fitattun jami’an da za su halarci babban taron kasa da kasa na DICAN da za a gudanar a Abuja a ranar 23 ga Yuli, 2025.

Taron wanda Ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu Rawaito Harkokin Diflomasiyya (DICAN) ta shirya, zai gudana a Rotunda Hall na Ma’aikatar Harkokin Waje tare da ministan harkokin waje Amb. Yusuf Tuggar, wanda shi ne babban mai masaukin baki, da zai gabatar da jawabin bude taron.

Taron zai duba matsalolin tsaro da suka shafi Najeriya da duniya gaba ɗaya, tare da tattauna dabarun diflomasiyya, leken asiri da rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Za a kuma tattauna kan tsarin manufofin diflomasiyyar gwamnatin Tinubu na “4Ds” wanda ya ta’allaka ne kan Dimokuraɗiyya, Ci gaba, kasashen ketare, da Ƙidayar Jama’a, domin fuskantar ƙalubalen tsaro na zamani da kyautata matsayin Najeriya a idon duniya.

Mahalarta taron sun haɗa da shugabannin ƙasa, gwamnoni, ‘yan majalisa, manyan jami’an tsaro, ƙwararru daga jami’o’i da cibiyoyin bincike, ɗalibai da sauran manyan baƙi daga cikin gida da wajen Najeriya.

Taron na DICAN na farko a irin sa, yana nuni da ƙudurin ƙungiyar wajen ƙarfafa haɗin gwiwa domin zaman lafiya da hana rikice-rikice, musamman a wannan lokaci da duniya ke fuskantar barazanar tsaro a yankuna kamar Gabas ta Tsakiya da Gabashin Turai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here