Koko da ƙosai Buhari yake ci a lokacin da yake mulkin Najeriya–Garba Shehu

0
16

Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙi amincewa da wani ƙudirin ƙarin kasafin kuɗi na Naira miliyan 10 da aka gabatar domin abinci a fadar shugaban ƙasa a lokacin mulkinsa.

Garba Shehu ya bayyana haka ne a cikin littafinsa mai suna “According to the President: Lessons from a Presidential Spokesperson’s Experience”, wanda aka ƙaddamar a birnin Abuja ranar Talata.

Littafin ya ƙunshi tarihin shekaru takwas da ya shafe yana aiki a ƙarƙashin Buhari, tare da bayani kan wasu sirrika da suka shafi tafiyar da mulki a fadar shugaban ƙasa na wancan lokaci.

A cewar Shehu, jim kaɗan bayan Buhari ya hau mulki a shekarar 2015, an shaida masa cewa akwai buƙatar ƙarin kasafin abinci zuwa Naira miliyan 10 domin ciyar da shugaban ƙasa, mataimakinsa, baƙi, da kuma bukukuwan gwamnati.

“Da suka ce za a kashe Naira miliyan 10, sai ya yi mamaki tare da buƙatar a rage kuɗin,” in ji Shehu.

Garba Shehu ya bayyana irin abincin da Buhari ke ci a kullum da cewa abinci ne mai sauƙi.

“A matsayinsa na shugaban ƙasa, yawancin abincin da Buhari ke ci abinci ne da talakawan Najeriya ke ci, kamar su tuwo, koko, da ƙosai, wake, alkama, kayan lambu masu yawa, kaji da naman raguna. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here