Cire tallafin fetur ya jefa yan Najeriya cikin ƙunci da yunwa—Atiku

0
14

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi tun ranar farko da ya hau mulki ya jefa ‘yan Najeriya cikin matsanancin halin tattalin arziki, yunwa da ƙuncin rayuwa.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, Atiku ya ce matakin ya kasance wanda aka ɗauka cikin gaggawa ba tare da zurfin tunani ba, inda ya zargi gwamnatin da saba alkawarin da ta ɗauka na ba da tallafin na wucin gadi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya domin rage tasirin cire tallafin.

Atiku ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki watanni 10 kafin ta cimma matsaya kan sabon mafi ƙanƙantar albashi, amma har yanzu ba a biya cikakken tallafin watanni 10 da aka yi alkawari ba, sai watanni shida kawai aka biya, bayan jinkiri da alkawura da ba a cika ba.

A ƙarshe, Atiku ya ce kowanne ma’aikaci na bin gwamnati bashin naira 140,000, wanda ya kunshi naira 35,000 na watanni huɗu da ba a biya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here