Rundunar ƴan sandan ƙasa ta tabbatar da tsaurara matakan tsaro a garin Zogirma, na ƙaramar hukumar Bunza, dake jihar Kebbi, bayan wani hari da ake zargin ƴan ta’addan Lakurawa ne suka kai, inda suka kashe jami’an ƴan sanda uku tare da jikkata fararen hula biyu.
Kakakin rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ya ce jami’an sun samu harin ne a hanyarsu daga Zogirma zuwa Tilli, inda aka yi musayar wuta da maharan.
Rundunar ta ce itama ta jikkata wasu daga cikin maharan.
A yanzu haka an tura ƙarin jami’an kwantar da tarzoma don tabbatar da zaman lafiya, yayin da Kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Muhammed Sani, ya kai ziyara yankin tare da tattaunawa da al’umma domin tabbatar da tsaro.