Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda, ya sanar da cewa iyalan marigayi tsohon shugaban ƙasa Buhari, sun tabbatar da cewa za’a yi jana’izar sa a birnin Daura dake jihar Katsina.
Radda, ya sanar da hakan a yammacin Lahadi lokacin da yake zantawa da manema labarai akan rasuwar Buhari. Yace tun a ranar Juma’a yaje Landan don duba lafiyar tsohon shugaban kasar, wanda ya rasu a daidai lokacin da yake niyyar dawowa Najeriya.
Muna sa ran za’a yi jana’izar sa a gobe Litinin zuwa La’asar in har komai ya tafi kamar yadda aka tsara, saboda mataimakin shugaban ƙasa zai iso Landan a wannan dare tare da tafiya da gawar zuwa safiya, inji Radda.
In har ba wata tangarɗa aka fuskanta ba zuwa La’asar za’a yi jana’izar a Daura, ya kara da cewa.