In abubuwa basu daidaita ba zamu sake yin Sallar Rokon Ruwa—Ibrahim Khalil

0
14

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim, ya nemi a’lumma su yawaita yin kyauta, sadaka tare da sauran ayyukan alkairi da niyyar Allah ya kawo saukar ruwan sama mai albarka, yalwar arziki da yayewar ƙunci a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Shugaban, ya bayyana hakan a yau Asabar bayan gudanar da Sallar Rokon Ruwan sama a masallacin Umar Bin Khattab, dake Shatale-talen Dangi a jihar Kano.

Malam Khalil, ya kuma nemi kowa ya gyara tsakanin sa da Allah, sannan kowa ya gyara tsakanin sa da mutanen da yake rayuwa dasu, inda yace duk wanda yasan yaci dukiyar ɗan uwansa yayi kokarin mayar masa da hakkin sa, don samun rayuwa mai kyau.

Bayar da sadaka ko kyauta na daga cikin abubuwan dake sanyawa Allah ya dena fushi da al’umma da kuma yalwata musu, inji Malamin.

Idan muka ga rashin ruwan saman ya cigaba da kasancewa duk da cewa munyi sallar rokon ruwan, zamu sake sanya lokaci don yin wata Sallar don neman yardar Allah.

Dr. Ibrahim Sale Kumurya, shine limamin daya jagoranci sallar, wadda al’umma da dama suka halarta, sannan shima ya nemi kowa ya ya rika kokarin sauke nauyin dake kansa, tun daga kan shugabannin al’umma har zuwa kan waɗanda ake jagoranta.

Limamin, yace rashin kiyaye dokokin Allah madaukakin sarki, na daga cikin abubuwan dake kawo rashin wadatar ruwan sama, da ƙuncin rayuwa.

Malaman Islama da jami’an gwamnatin jihar Kano, da fitattun mutane sun halarci sallar cikin su harda Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, Sha’aban Ibrahim Sharada, da Ali Muhammad Bichi, mai bawa gwamnan Kano shawara akan harkokin addini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here