Direba Ya Gudu Da Buhunan Masara 463 Bayan Ya Bai Wa Ɗan Rakiyarsa Guba

0
24

Ana zargin wani direban tirela da sace buhunan masara guda 463 da aka dora masa domin kaiwa kamfani, bayan da ya ba wa ɗan rakiyarsa shayi mai guba a yankin Maraban Jos, Jihar Kaduna.

Injiniya Jamilu Haruna, wani ɗan kasuwa da ke safarar hatsi daga Kano zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan, ya shaida wa jaridar Aminiya cewa ya ɗora wa direban buhunan masara ne domin kai su kamfanin Olam da ke Ilorin, Jihar Kwara.

“Jimillar kuɗin kayan ya kai naira miliyan 21 da dubu 686 da ɗari huɗu. Wannan dukiya tawa ce gaba ɗaya da na dora a wannan mota mai taya 18,” in ji shi.

Ya ce direban ya sami nasarar sace kayan ne ta hanyar shan shayi mai guda wanda ya bawa ɗan rakiyarsa, sai dai daga bisani ya farka cikin galabaita, sannan ya gano an tsere da motar da kayan cikinta.

Mun sanar da jami’an tsaro ciki har da ’yan kamasho da ke da masaniya kan masu haya irin wannan. Haka nan ’yan sanda sun shiga bincike, amma har yanzu ba a gano direban ba,” in ji Jamilu.

Ya ce lamarin ya jefa shi cikin halin tabarbarewa tattalin arziki domin kuwa ya rasa duk jarin da yake juyawa, kuma har yanzu ba wani cigaba da aka samu kan gano motar ko direban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here