Tinubu ya tura Shettima ya duba lafiyar Buhari a sirrance

0
8

Rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima, a ɓoye zuwa London domin ya ziyarci tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ke jinya a wani asibiti.

Shettima yaje ziyarar daga Addis Ababa, inda ya halarci wani taro a madadin Najeriya, amma daga bisani Tinubu da ke wata ziyara a St Lucia ya umurce shi da ya wuce London ya duba lafiyar Buhari.

Mai magana da yawun Shettima ya tabbatar da ziyarar, amma ya ce bai san cikakken dalilinta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here