Rundunar ƴan sandan Kano taja kunnen al’umma akan wa’azin Malam Lawan Triumph

0
18

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa tana sane da takaddamar da ta ɓarke sakamakon wasu kalamai a cikin wa’azin Sheikh Lawal Triumph, wanda ya janyo muhawara da sa-in-sa a tsakanin al’umma.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a yau Juma’a, rundunar ta jaddada cewa kowa na da ƴancin faɗar albarkacin bakinsa, amma wajibi ne a tabbatar da cewa ana yin hakan cikin doka da oda.

Sanarwar ta bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar ya gayyaci Sheikh Lawal Triumph, domin tattaunawa tare da wasu masu ruwa da tsaki a Kano, ciki har da jami’an gwamnati da shugabannin addinai da na al’umma. Wannan mataki, a cewar rundunar, na da nufin dakile ci gaba da bazuwar irin wannan rikici a nan gaba.

Rundunar ta bukaci al’umma da su kwantar da hankali tare da gujewa daukar matakan da ka iya haifar da rikici. Ta kuma shawarci jama’a da su rika gabatar da koke-kokensu ta hanyar da ta dace, maimakon amfani da kafafen sada zumunta wajen tayar da hankali.

Rikicin ya samo asali ne daga wani wa’azi da Sheikh Lawal Triumph ya gabatar, inda ya bayyana cewa kwarkwata ba kazanta ba ce ga Larabawa, a wani martani ga masu kalubalantar ingancin hadisin da ke cewa kwarkwata kazanta ce. Wannan kalamai ne suka haifar da zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta, har wasu ke yin kiraye-kirayen daukar matakin kai tsaye a kan malamin bisa zargin batanci.

Rundunar ta jaddada cewa dole ne a mutunta bambancin ra’ayi da fahimta tsakanin al’umma, amma a dinga yin hakan ba tare da karya doka ko tayar da hankali ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here