Wasu lauyoyin gwamnatin Kano da suka nemi a sakaya sunan su sun koka bisa yadda suka zargi kwamishinan shari’a da mayar musu da aiki baya, tare da cin dunduniyar su.
Wadannan lauyoyi sun bayyana fushin su akan cewar kwamishinan shari’a na jahar Kano ya hana su hakkokinsu daya Æ™unshi rigar zuwa kotu da hula da kuma na’ura mai kwakwalwa wadda gwamnan Kano yace a basu don inganta gudanar da aiki.
Wadannan lauyoyi dai sun bayyana cewar suna daf da tsunduma yajin aiki sakamakon zargin cin dunduniyar da ake yi wa aikins.
Wata majiya ta bayyana cewar da zarar an kawo takardun tuhuma akan zargin manyan laifukan kamar fyade ko kisan kai ko fashi da makami, bayan kammala bincike sun kuma samu mutum da laifi a wasu lokutan sai ayi umarnin a saki wanda ake zargin maimakon a kai shi kotun da ta ke da hurumin yi masa Shari’a.
Bayan Jin wannan zarge-zargen muka tuntubi kwamishinan shari’ar don jin ta bakin sa amma ya umarci babban sakatare a ma’aikatar shari’a Barrister Mustafa Muhammad Nuraddin, ya yiwa manema labarai karin haske dangane da zarge zargen inda yace zargin lauyoyin ba gaskiya bane.