Kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmad Musa, ya bayyana cewa hukuncin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za ta yanke kan wasan da aka buga tsakanin Afirka ta Kudu da Lesotho ne kawai ragowar damar da Najeriya ke da ita akan zuwa gasar cin kofin duniya ta shekara mai zuwa a ƙasashen Amurka, Kanada da Mexico.
“Mu a yanzu muna cikin mawuyacin hali, sai dai mu ce sai ikon Allah ne kaɗai zai sa Najeriya za ta samu damar zuwa gasar cin kofin duniya,” in ji Musa.
Ahmad Musa ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na farko da ya gudanar a matsayinsa na sabon Babban Manajan ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Kano Pillars.
Ya ce idan FIFA ta soke nasarar da Afirka ta Kudu ta samu a hannun Lesotho, hakan zai iya dawo da wani ƙaramin fata ga Najeriya ta samu gurbin shiga gasar.
Musa ya kuma bayyana ƙalubalen da Kano Pillars ta fuskanta a kakar wasan da ta gabata ta gasar Premier League ta Najeriya (NPFL), inda ya ce yanzu ƙungiyar za ta mayar da hankali wajen neman kamfanoni masu daukar nauyi maimakon dogaro kacokan da tallafin gwamnati.
Sabon babban manajan ya kuma ce suna da shirin ɗaukar ƙwararrun ‘yan wasa daga ƙasashen waje da kuma ƙara inganta ƙwarewar ‘yan wasan cikin gida domin samun nasara a sabon zangon kakar wasa.
Ahmad Musa ya roƙi haɗin kan kafafen yaɗa labarai domin cimma burin da aka sa gaba a ƙungiyar.