Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta fara shirye-shiryen aikin hajjin shekarar 2026, bayan kammala aikin hajjin bana.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Pakistan, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis a Kano.
Ya ce hukumomin Saudiyya sun bukaci kowace ƙasa da ta fara shirye-shiryenta tun da wuri, domin ba za su yarda da jinkiri ba a wannan lokaci.
Farfesa Pakistan ya ce abin da ya rage yanzu shi ne amincewar hukumomi kan kuɗin kujerun hajjin 2026, domin a sanar da alhazai su fara biyan kuɗin.
A hajjin da ya gabata, maniyyatan Najeriya sun biya sama da naira miliyan takwas a matsayin kuɗin aikin hajji.
Ya kuma yi kira ga masu niyyar zuwa hajji a badi da su shirya kuma su hanzarta biyan kuɗi da zarar an bayyana farashin kujeru.