Dangote yace matatun fetur na gwamnatin Najeriya ba zasu taɓa yin aiki ba

0
9
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ba ya ganin matatun man gwamnati da ke Port Harcourt, Warri da Kaduna za su iya dawowa aiki yadda ya kamata.

Ya ce an kashe sama da dala biliyan 18 a kan matatun da ke karkashin NNPC, amma har yanzu ba sa aiki.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙi daga makarantar koyon harkokin kasuwanci dake Lagos, a sabuwar matatar man sa da ke Lekki, inda ya ce matatar Dangote na tace fiye da kashi 50% na man fetur, yayin da matatun gwamnati ke iya kashi 22% ne kawai.

A cewar Dangote, gyaran matatun gwamnati tamkar gyara motar da aka kera shekaru 40 da suka wuce ne, duk da cigaban fasaha da aka samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here