An kama magungunan jabu da kuɗin su zarce Naira biliyan 1 a jihar Kano

0
13

Hukumar kula da harkokin magunguna a cibiyar siyar magani ta Kanawa, da ke jihar Kano, ta samu nasarar kama magunguna na jabu da waɗanda basu da inganci da aka kiyasta darajarsu da cewa takai naira biliyan 1 da miliyan ɗari 3.

Cibiyar, wacce ita ce irinta ta farko a Najeriya, an samar da ita domin dakile sayar da magunguna a kasuwanni barkatai, da hana siyar da magani ba bisa ka’ida ba.

Da take bayani a wani taron taron manema labarai, shugabar ma’aikatan cibiyar, Furera Muhammad, ta bayyana cewa yawancin magungunan da aka kama sun haɗa da na zazzaɓin cizon sauro, da sauran magunguna waɗanda ake buƙatar su sosai a kasuwa.

Ta ce binciken dakin gwaje-gwaje ya nuna cewa magungunan sun gaza cin gwajin da ke tantance adadin sinadarin maganin da ya kamata su ƙunsa.

Hukumar tace yanzu haka suna da cikakken iko da kulawa kan harkar rarraba magunguna a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here