An gurfanar da wata Amarya mai suna Saudat Jibril, a gaban babbar kotun jihar Kano bisa zargin aikata laifin kisan mijinta bayan mako ɗaya da yin auren su.
An gurfanar da Amaryar a babbar kotun dake karkashin jagorancin mai sharia Maryam Sabo.
Saudat Jibril, ta kasance yar unguwar Farawa dake birnin Kano, inda ta musanta aikata laifin kisan mijin nata bayan, bayan jami’in kotun Auwal Garba, karanto abin da zargin ta da aikatawa.
Mai gabatar da Kara Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya gabatarwa da kotu shaida wato dan sandan da yayi binciken laifin mai suna Supeta Ijibtil, kuma yayi bayani dalla dalla, sannan Lauyan dake tsaya mata yayi masa tambayoyi, da hakan yasa kotun ɗage cigaba sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga watan da muke.
Ana dai zarginta da kashe angonta wato Salisu Idris, bayan mako guda da daura musu aure, inda akace tayi amfani da wani abin sha mai ɗauke da guda tare da caccaka masa wuka, kuma ya mutu sanadiyar hakan.
Zuwa yanzu dai an tafi da ita zuwa gidan gyaran hali kafin lokacin cigaba da shari’ar.