Ambaliya Ta Rusa Gidaje Fiye da 200 a Jihar Kebbi

0
8

Fiye da magidanta 200 ne suka rasa matsugunansu bayan wata mummunar ambaliya ta afkawa ƙauyen Zogirma da ke ƙaramar hukumar Bunza a jihar Kebbi.

Ambaliyar, wadda ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama, ta lalata gidaje, gonaki, shaguna da sauran dukiyoyi masu yawa. 

Wannan lamari ya jefa daruruwan mazauna yankin cikin halin ƙaƙanikayi, inda da dama ke neman mafaka.

A farkon wannan mako ne hukumar hasashen yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya a wasu sassan ƙasar nan sakamakon tsananin ruwan sama da ake sa ran zai zuba a damunar bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here