Zan sake doke Matawalle a zaɓen 2027 kafin goma na safe—Gwamnan Zamfara

0
23

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa yana shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. A cewarsa, yana da tabbacin cewa zai sake kayar da wanda ya gada, Bello Matawalle, a zaben 2027, kafin ƙarfe goma na safe a ranar zabe.

Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels a ranar Laraba, Gwamna Lawal ya ce yana yin biyayya ga jam’iyyar PDP, kuma bai da wani shirin sauya sheƙa.

Lawal ya bayyana cewa kiraye-kirayen da yake samu daga APC da wasu ‘yan siyasa wani salo na karkatar da hankali, yana mai cewa irin waɗannan ƙungiyoyin siyasa ba su hana shi samun nasara a zaɓen 2023 ba.

“A lokacin da na tsaya takara a 2023, dukkan waɗannan manyan ’yan siyasar na Zamfara suna tare a APC, irin su Sani Yerima, Mahmuda Aliyu Shinkafi, Abdulaziz Yari, da Matawalle, amma duk da haka na ci zabe,” in ji shi. “Ba na jin tsoronsu a 2027. Iko daga Allah ne kawai.”

Game da rahotannin da ke cewa yanzu karamin Ministan Harkokin Tsaron, Bello Matawalle, yana shirin komawa takara a 2027, Lawal ya ce yana maraba da hakan.

“Ina roƙon Allah Matawalle ya fito takarar APC a 2027. Sai mu ga yadda za ta kaya,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here