Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana mamakinsa kan yadda shugaban Liberia, Joseph Boakai, ke iya magana da harshen Turanci cikin ƙwarewa.
Trump ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba yayin da yake karɓar baƙuncin shugabannin ƙasashen Gabon, Guinea-Bissau, Liberia, Mauritania, da Senegal a fadar White House.
A yayin ganawar, Trump ya tambayi Boakai inda ya koyi Turanci, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta da wasu kafafen watsa labarai.
Wasu na kallon kalaman Trump a matsayin nuna wariyar launin fata da kuma cin mutuncin shugaban Liberia.
Wata ‘yar majalisar dokokin Amurka baƙar fata, Jasmine Crockett, ta bayyana hakan a matsayin abin kunya da raini ga dukkan nahiyar Afrika.