Taimakon Tinubu ne yasa Buhari zama shugaban ƙasa—Hadimin Tinubu

0
11

Mai taimakawa Shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai, Temitope Ajayi, ya mayar da martani kan kalaman tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, wanda ya ce Bola Ahmed Tinubu bai taka rawa wajen samun nasarar Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2015 ba.

A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Ajayi ya bayyana cewa duk da cewa Buhari na da kuri’un Arewa miliyan 12, amma ya sha kaye a zaben shugaban kasa na 2003, 2007 da 2011 kafin ya samu nasara a 2015.

Ajayi ya kara da cewa da ba dan irin goyon bayan da Bola Tinubu ya bayar ba a zaben fidda gwanin jam’iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na Teslim Balogun a Legas a 2014, inda ya hada kai da gwamnoni da wakilan yankin Kudu maso Yamma don mara wa Buhari baya da wuya ya samu tikitin takarar shugaban kasa.

Ajayi ya zargi Boss Mustapha da yiwa tarihi na baya-bayan nan babban lahani, inda ya rubuta cewa mu bar batun babban zabe na 2015 da Buhari ya samu nasara. A dubi yadda aka kai ga samun wannan nasara tun daga matakin zaben fidda gwani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here