Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’addan Boko Haram 24 a Jihar Borno

0
12
Sojoji
Sojoji

Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ƴan ta’addan Boko Haram guda 24 a wasu jerin hare-haren hadin gwiwa da suka gudanar a sassa daban-daban na Jihar Borno.

Wannan jawabi ya fito cikin wata sanarwa da mai rikon mukamin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Kasa a Hedikwatar Rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa, hare-haren da aka kai daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Yuli sun kasance hadin gwiwa ne tsakanin bangarorin sojin kasa da na sama na rundunar OPHK, da ‘yan sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF), da kuma masu farauta.

Dakarun sun aiwatar da wadannan hare-hare a kauyuka da dama da suka hada da Platari, Komala, Kawuri, Madarari, Leno Kura, Sabsawa, Ngoshe-Gava, Ngoshe-Ashigashiya, Amuda-Gava, Pambula, Tangalanga, Bula Marwa, Ngailda, Manjim, da Wulle.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here