Sabbin mutane miliyan 6 zasu kamu da cutar HIV—Majalisar ɗinkin duniya

0
13

Shirin Majalisar Dinkin Duniya kan cutar HIV/AIDS (UNAIDS) ya yi hasashen cewa mutane miliyan shida za su iya kamuwa da cutar HIV, tare da mutuwar mutum miliyan hudu nan da shekarar 2029, idan aka dakatar da tallafin da Amurka ke bayarwa don yaƙi da cutar.

A yau Alhamis ne ake sa ran Shirin zai fitar da rahoton sabbin alkaluma kan yawaitar kamuwa da cutar a faɗin duniya.

Afrika ta Kudu ce ƙasar da ta fi yawan masu ɗauke da cutar HIV a duniya, kuma ita ce ta fi cin gajiyar tallafin Amurka kafin watan Maris na bana.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa tallafin Amurka ya taimaka matuƙa, inda ya rage yawan sabbin kamuwa da cutar da kashi 60 cikin 100 tun daga shekarar 2000, zuwa yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here