Najeriya na cikin tsaro mai inganci da kwanciyar hankali–Ribadu

0
10

Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi kira ga masu sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su daina raina jajircewar shugaban wajen ceto Najeriya daga matsalolin da take fuskanta.

Ribadu ya bayyana hakan ne a yayin wani taron kasa da kasa kan tsaron yanar gizo (Cybersecurity Conference) na shekarar 2025 da aka gudanar a Abuja.

A cewarsa, Najeriya na cikin yanayi mai kyau ta fuskar tsaro da kwanciyar hankali, tare da jawo hankalin masu zuba jari daga cikin gida da waje sakamakon gyare-gyaren da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa tun daga hawansa mulki.

Ya soki wasu daga cikin masu sukar gwamnati da ya ce yawanci tsoffin ‘yan siyasa ne da suka rasa tasiri, amma suke Æ™oÆ™arin ci gaba da bayyana kansu a matsayin masu muhimmanci, duk da cewa basu da wani sabbin tsare-tsare ko gudummawa da za su iya kawo ci gaba ga kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here