Majalisar Malaman Kano Ta Kira Al’umma Zuwa Sallar Roƙon Ruwan Sama

0
8

Majalisar Malaman Jihar Kano ta bukaci al’ummar jihar da su fito domin halartar sallar roƙon ruwan sama, duba da yadda damuna ke kankama amma ana fuskantar ƙarancin ruwa.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban majalisar, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sanya wa hannu, wadda sakataren majalisar, Dr. Saeed Ahmad Dukawa, ya aikewa manema labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa, majalisar ta yanke shawarar gudanar da wannan sallah saboda ƙarancin ruwan sama da ake fuskanta a bana, duk da cewa lokacin damuna yayi nisa.

Majalisar ta yi kira ga al’umma da su fito da zuciya ɗaya da niyyar neman rahamar Allah da albarkarsa a wannan lokaci.

An shirya gudanar da sallar roƙon ruwan saman ne a ranar Asabar, 12 ga watan Yuli da ƙarfe 9 na safe, a masallacin Juma’a na Umar Bin Khattab da ke kan titin zuwa Zariya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here